Barka da war haka. Barka da shiga darasin sakar-kasa-da-kasa, tarihi, kimiyya da tsaro. Suna na Charles (Chals) Nine zan zama jagora a wannan darasi. Don haka bisimillah. Wa nake tunanin ya dace da wannan darasin? jawabi shine kai, Yakamata ka dauki wannan darasi. Domin kowa ma yakamata ya dauki wannan darasin tufkar-aiki da muke iya tabawa mu kuma yi amfani da ita yana tare damu a kowane lokaci. A bayyane take, idan kana kallon wannan darasi. Kana kallon ne bisa sakar-kasa-da-kasa. ta yaya ne wadannan abubuwa suke aiki? ka sani? wannan fa ba akan bishiyoyi ya tsiro ba Mutane ne suka samar da shi, tabbas ! za kuma mu yi magana ne akan abu mai zurfin bayani Watakila ma abinda ya fi komai cukurkudewa a kimiyance, watakil, amma baza mu yi magana ba ne ta mahangar lissafi, kuma baza muyi magana ta mahangar manhajar naura mai kwakwalwa ba. Abinda nake nufi shine baza mu matsa maka ba ta wannan bangaren. Za muyi magana ne akan abubuwan ban sha'awa a kimiyance, za mu hadu da wadansu mutane ma su ban sha'awa, amma wannan darasi ba a zufafan ma'ana za mu koyar da shi ba, darasi ne akan sauraro da fahimta da kuma zufafa tunani akan wadannan mutane wadanda suka mayar da sakar-kasa-da-kasa abinda ta zama.